
Na Yafe Duk Wata Rashin Fahimta Da Ta Shiga Tsakanina Da Marigayi Sheik Idris Dutsen Tanshi, Inji Gwamna Bala Mohammed
…Malami ne mara tsoro da ya sadaukar da rayuwarsa wajen karantar da mušùĺùnçìn, wanda jihar Bauchi za ta yi kewarsa
…ya ku mallakawa Almajiransa filin game village
Daga Rariya
A yammacin yau Abasar ne Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed ya kai ziyarar ta’aziyyar rasuwar Sheik Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ga iyalansa da mabiyansa, wanda ya rasu a daren Juma’ar da ta gabata.
Gwamna Bala wanda ya jagoranci tawagar mukarraban gwamnati, ya kai ziyarar ta’aziyyar ne a madadin kansa, iyalansa, gwamnati da kuma daukacin al’ummar jihar Bauchi.
Gwamnan ya bayyana marigayi Shehin Malamin a matsayin malamin mara tsoro wanda ya sadaukar da kansa wajen karantar da addìnìn musulunci, shari’a da kuma doka. Inda ya ce jihar Bauchi ta yi rashin gwani, masani kuma fasihi.
Gwamnan ya yi fatan Allah ya jikan Sheik Idris Dutsen Tanshi ya sa shi a aljannatul firdausi, Ya kuma baiwa iyalansa hakurin jure rashin.
A yayin ziyarar jajen, Gwamna Bala ya kuma sadaukarwa mabiyan Malamin filin idi na game village. Ya kuma bayyana cewa ya yafe duk wani rashin fahimata da ya shiga tsakaninsa da marigayin.
Da yake jawabi a madadin iyalan mamacin da kuma al’ummar musulman yankin, Malam Ya’u da Alhaji Shehu Barau Ningi sun mika godiyar su ga Gwamnan bisa ziyarar da ya kawo da kuma irin kalaman da ya yi.
Shehu Barau ya kuma bayyana muhimmancin sake mallaka musu filin na game village, wanda marigayin ya jima yana fatan mallaka.
Daga Lawal Muazu Bauchi
Mai taimakawa Gwamna Bala
Kan harkokin kafafun sadarwar zamani
05/04/25