
Tsohon gwamnan jihar Kaduna malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa yayi iya lissafinsa bai ga ta yanda shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai sake con zabe ba a 2027.
Ya bayyana hakane hirar da aka yi dashi a Channels TV inda yace Tinubu na 3 zaizo a zaben.
Yace amma akwai yiyuwar za’a yi saben zagaye na biyu dan da wuya a samu wanda yayi nasara a zagayen farko.