Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, zai mayar da Najeriya kamar kasar China.
Shugaban ya bayyana hakane bayan ziyarar da ya kai kasar ta China inda ya gana da shugaban kasar, Xi Jinping.
Ya bayyana hakane a taron da yayi da ‘yan Najeriya mazauna kasar ta China.
Shugaban yace, Najeriya na bukatar da’a da jajircewa irin ta kasar China inda yace a hakane zata cimma burinta kuma a rika girmamata a idon Duniya.