
Kungiyar SERAP dake saka ido kan yanda ake kashe kudin gwamnati ta nemi gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta dakata da karbo bashin Dala Biliyan 1.08 da take shirin yi.
Maimakon hakan, Kungiyar ta yi kira ga gwamnatin Tinubu data yi binciken zargin batan makudan kudaden da suka kai Naira Biliyan 233 da ake yi a ma’aikatar wutar lantarki ta Nigerian Bulk Electricity Trading Plc., Abuja.
SERAP tace kamata yayi a bincika idan aka samu gamsassun hujjoji game da lamarin duk wanda aka samu da laifi a hukuntashi.
Sannan kuma tace idan aka kwato kudaden a yi amfani dasu wajan cike gibin kasafin kudin shekarar 2025.
A satin da ya gabata ne dai bankin Duniya ya amince ya baiwa Najeriya bashin Dala Biliyan $1.08 dan amfani da kudin wajan inganta ilimi da gina gidaje da samar da abinci me gina jiki ga mutane.
Saidai a sanarwar da kungiyar SERAP ta fitar tace karbo wannan bashi ba dole bane ga Najeriya sai ma durkusar da kasar da zai kara yi.
A shekarar 2021 ne dai aka nemi ba’asi game da kudaden da hukumar ta NBET ta kashe wanda aka kasa samu.
SERAP tace ta baiwa Gwamnati nan da kwanaki 7 ta bata amsa game da fasa karbo bashin har sai an kwato wadancan kudade, kungiyar tace idan bata ji wata gamsashshiyar amsa nan da karshen kwanaki 7 din ba zata garzaya kotu.