
Malamin Kirista, Primate Elijah Ayodele ya bayyana cewa, Naira Miliyan 150 ko takalmi ba zata sai mai ba.
Ya bayyana hakane a cocinsa sannan a matsayin martani ga Ministan wuta, Bayo Adelabu wanda ke son tsayawa takarar gwamnan jihar Oyo.
Shi dai Ministan ya zargi malamin da cewa ya nemi ya bashi Naira Miliyan 150 ya masa Addu’ar neman nasara amma ya kiya shine ya koma yana bata masa suna.
Saidai Faston yace kawai Bayo Adelabu yaga ba zai yi nasara bane a zaben me zuwa shine yake soki burutsu.