
Babban fasto a kudancin Najeriya da yake yawan jawo cece-kuce, Odumeje ya bayyana cewa, ya je kasar Amurka amma bai ga tafi Najeriya da komai ba.
Wannan kalamai nasa sun jawo cece-kuce sosai a tsakanin al’umma inda wasu suka rika yaba masa da kishin kasa daya nuna amma wasu suka ce ikirarin sa ba gaskiya bane.
Shi dai Fasto Odumeje ya nuna alfahari da kasarsa sosai.