Friday, December 5
Shadow

Najeriya ce kasa ta 12 mafi talauci a Duniya>>Inji IMF

Rahotan kungiyar bayar da lamuni ta Duniya, IMF yace Najeriya ce kasa ta 12 mafi yawan talakawa a Duniya.

An yi amfani da alkaluma GDP per Capital ne wajan fitar da wadannan bayanai, watau yawan kudaden da kowane dan kasa ke samu a shekara.

Rahoton yace kowane dan Najeriya na samar da akalla dala $807 kowace shekara.

Kasar Sudan ta kudu ce ta daya sai Yemen, Burundi, the Central African Republic da Malawi.

Sauran kasashen sune Madagascar, Sudan, the Democratic Republic of Congo, Mozambique da Jamhuriyar Niger.

Kasar India ma ta zo a matsayi na 50 a cikin kasashen da suka fi talauci a Duniya.

Karanta Wannan  A shirye nake in auri Maryam Sanda bayan da shugaba Tinubu ya mata Afuwa>>Inji Matashi, Sarki

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *