
Rahotanni sun bayyana cewa Najeriya ta zo ta 3 a jerin kasashe 10 mafiya yawan masana’antu a Nahiyar Afrika.
Kafar The African Exponent ce ta wallafa wannan bayani.
Kafar tace ta yi binciken nata ne aka shekaru 10 da suka gabata inda ta bayar da muhimmanci ga kasashen dake da masana’antu mafiya yawa dake samar da abubuwan amfani.
Jadawalin kasashen sune kamar haka:
South Africa; Egypt; Nigeria; Morocco; Kenya; Algeria; Ethiopia; Ghana; Tunisia; and Zambia.