Hukumar yaƙi da safarar mutanen da Najeriya, NAPTIP, reshen jihar Kano ta ce ta kuɓutar da wasu mutum 285 da aka yi yunkurin safararsu tare da kama masu safarar 22 a shekarar 2024.
Kwamandan hukumar a reshen jihar, Abdullahi Babale ne ya bayyana haka cikin wata hira da kamfanin dillancin labaran ƙasar NAN a Kano.
Babale ya ce daga cikin mutum 285 da aka kuɓutar, 78 maza ne, yayin da 97 daga ciki mata ne, da ƙananan yara 110.
Yayin da babban jami’in hukumar a jihar Kano ya ce sun kama mutum 22 bisa zargin hannu a laifin ciki har da maza takwas da mata 14.
Abdullahi Babale ya ce laifukan da ake zarginsu sun haɗa da cin zarafin ƙananan yara da tilasta musu aikin ƙarfi, da cin zarafi ta hanyar lalata da sauran laifuka ƙarƙashin dokokin cin zarafin ɗan’adam.