Thursday, January 15
Shadow

Nasan Gyare-Gyaren da nake sun jefa ‘yan Najeriya a wahala amma nan gaba za’a ga alfanunsu, Ku dauka kamar maganine me daci, idan za’a sha ba dadi amma ana samun waraka>>Shugaba Tinubu

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, yasan Gyare-Gyaren tayar da komadar tattalin arziki da yake yi sun jefa ‘yan Najeriya a rayuwar wahala.

Yace amma maganar gaskiya gyaran ya zama dole kuma nan gaba za’a ga amfaninsa.

Shugaban ya bayyana hakane a yayin ganawar da yayi da ‘yan Najeriya mazauna kasar Brazil inda ya nemi hadin kansu wajan ciyar da Najeriya gaba.

Ya kuma nemi a hada kai dan zaman lafiya da kawo ci gaba ga Najeriya.

Karanta Wannan  Bill din wuta da akw kawo mana yayi yawa ba zamu iya biya ba shiyasa zamu koma amfani da Sola>>Inji Fadar shugaba Tinubu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *