
Kotun daukaka kara a Abuja ta yi watsi da bukatu guda biyu da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya shigar, tare da yanke masa hukuncin biyan tara na naira 100,000.
Kwamitin alkalai uku na kotun, wanda Mai Shari’a Hamman Barka ke jagoranta, ne ya yanke hukuncin a ranar 21 ga Mayu, 2025, bayan Akpabio ya nemi a janye karar da ya shigar.
Kotun ta kuma tabbatar da sahihancin kwafin hukuncin.
Bukatun da aka yi watsi da su an shigar da su ne a ranar 3 ga Maris, 2025, da kuma 25 ga Maris, 2025, kuma suna dauke da lambar shari’a CV/395/M1/2025 da CV/395/M2/2025, inda Akpabio ya kasance mai daukaka kara.