
Tauraron Tiktok, Gfresh Al-amin ya bayyana cewa, Yayi Shaharar da ba zai taba yin Taĺauci ba.
Ya bayyana hakane a shafinsa na Tiktok yayin da wasu ke masa dariyar wai an kulle Tiktok live dan haka ya daina samun kudi.
Yace shi yayi shaharar da yana samun kamfanoni da yakewa talla dan haka ko ba Tiktok live zai ci gaba da rayuwar jin dadi.
Ya kara da cewa babban abinda ya bashi mamaki shine cikin masu murnar zai daina samun kudi saboda an dakatar da Tiktok live hadda tsohuwar matarsa Maryam.
Yace wallahi da yayi niyyar bata kyautar Naira Miliyan 1 dan baya so ta shiga wahala amma yanzu ya fasa