
Tsohon shugaban kamfanin mai na kasa, NNPCL, Mele Kolo Kyari ya bayyana cewa ya gudanar da aikinsa da tsoron Allah a zuciya.
Yace a shirye yake ya amsa tambayoyin EFCC dan yasan Akwai tambayoyin Allah ma da zai amsa.
Ya bayyana hakane a martanin da yayi ta X kan cewa, EFCC sun kamashi.
Mele Kyari yayi kira ga kafafen yada labarai da su guji yada labarin da bai inganta ba.