
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana hadakar da manyan ‘yan Adawa suka yi da taron wanda damuwa tawa yawa.
Ya bayyana hakane ta bakin kakakinsa, Bayo Onanuga.
Hakan na zuwane bayan da Atiku Abubakar, Nasiru Ahmad El-Rufai, Rotimi Amaechi, Peter Obi, Kayode Fayemi da sauransu suka hada kai suka ce zasu kayar da Tinubun a zaben shekarar 2027.
Sanarwar ta fadar shugaban kasa ta bayyana hadakar ‘yan Adawar da cewa masu son kansu ne kawai ba masu kishin al’umma ba.
Ya kuma bayyana cewa ci gaban kasa ne Bola Ahmad Tinubu ya saka a gaba, kuma shi kadai ne zai iya kawo ci gaban dan haka ba zai bari wasu taron sakarkaru su dauke masa hankali game da aikin da yake ba.