Friday, December 5
Shadow

Obi ya koka kan rushe ginin ƙanin sa a Legas

Obi ya koka kan rushe ginin ƙanin sa a Legas

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, ya yi Allah-wadai da rushe wani gini da ya ce na ƙaninsa ne da ke jihar Legas.

Ya bayyana wannan mataki a matsayin abin da ya saɓa wa doka kuma yana nuna yadda Najeriya ke ƙara nutsewa cikin rashin bin doka a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Obi ya yi wannan furuci ne a lokacin da ya kai ziyarar gaggawa zuwa wurin da aka rushe ginin, inda ya nuna ɓacin ransa kan “take hakkokin ‘yan ƙasa da rashin bin ka’ida da aka yi ba tare da wata hujja ba.”

Karanta Wannan  Bidiyon wani mahajjacin Najeriya na kiran Shehu a Kasar Saudiyya ya jawo cece-kuce

Daily Trust ta rawaito cewa Obi ya ce jami’an tsaro sun hana ɗan’uwansa samun damar ceto duk wani kayan da ke cikin ginin kafin a fara rushewar.

Ya ƙara da cewa wannan abin da ya faru hujja ce ta yadda tsarin mulki ke tauye ‘yancin mutane ba tare da an ɗauki matakin da ya dace ba, kuma hukumomi na aiki ba tare da ladabtarwa ko ɗaukar alhaki ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *