Sunayen Allah (99) Tare Da Fa’idar Kowane Suna Da Kuma Yadda Za A Yi Amfani Da Shi
KARANTA KA KARU
Huwaallahul ladhii laa ilaaha illaa huwa.
Da sunan Allah mai Rahama Mai Jin kai.
Sunnar ma'aiki, Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam ta sanardamu cewa duk wanda ya haddace kyawawan sunayen Allah madaukakin sarki zai shiga Aljannah.
Bukhari da Muslim sun ruwaito daga Abu Huraira cewa, Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam yace, Allah na da sunaye 99, duk wanda ya haddacesu zai shiga Aljannah.
Hadisin sama na dauke da abubuwa 3:
Haddace sunayen Allah.
Da kuma fahimtar ma'anarsu.
Da aiki da abinda suka kunsa.
To idan mutum yasan Allah daya ne, ba zai hadashi da kowa ba wajan bauta.
Idan mutum yasan Allah ne me bayarwa, ba zai nema wajan wanin Allah ba.
Idan mutum yasan Allah me Rahama ne, zai aikata ayyukan da zasu sa ya samu rahama...