
Ministan Abuja, Nyesom Wike ya ce babbar jam’iyyar hamayyar ƙasar, PDP ba ta da kyakkyawan shiri da tsarin kayar da APC a zaɓen 2027 ba.
Yayin da yake jawabi a wata ganawa da manema labarai a Abuja, ranar Juma’a, tsohon gwamnan na jihar Rivers ya ce a yanayin da jam’iyyar PDP ke ciki a halin yanzu ba za a ce ta shirya wa zaɓen 2027, saboda rikicin shugabanci da jam’iyyar ke ciki.
”PDP ba ta shirya wa zaɓen 2027 ba, wannan a bayyane yake. Ga yadda suke tafiya a yanzu rikicin jagoranci na ci gaba da yi wa jam’iyyar tarnaƙi”, in ji shi.
A baya-bayan nan dai wasu daga jam’iyyun hamayyar ƙasar ciki har da PDp na ƙoƙarin samar da wata haɗaka domin tunkarar APC a 2027.
To sai dai da alama tafiyar na ci gaba da fuskantar tasgaro, saboda muradun wasu ƴansiyasar.