
Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa hadakata tsakanin Atiku Abubakar da Peter Obi da Malam Nasiru Ahmad El-Rufai zai baiwa ‘yan adawa nasara akan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a zaben shekarar 2027.
Mataimakin shugaban matasa na jam’iyyar na kasa, Hon. Timothy Osadolor ne ya bayyanawa jaridar Vanguard hakan a wata ganawa da ta yi dashi.
Yace Musamman Atiku Abubakar da Peter Obi idan suka hade kaga ana da jimullar kuri’u Miliyan 13 kenan inda shi kuma shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ke da kuri’u Miliyan 8.
Yace a haka tun karfe dayan rana zasu kayar da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a ranar zabe.