Friday, January 2
Shadow

PDP ta gargaɗi mambobinta kan goyon bayan Tinubu a 2027

Babbar jam’iyyar hamayya ta PDP a Najeriya ta gargaɗi mambobinta da ke nuna goyon bayan sake zaɓen Shugaba Tinubu na APC a 2027.

Cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran jam’iyyar Hon. Debo Ologunagba ya fitar, PDP ta bayyana hakan da ta ce wasu mambobinta na yi a matsayin yi mata zagon-ƙasa.

”Abin taƙaici ne abinda wasu mambobinmu ke yi a kafafen yaɗa labarai, inda maganganunsu da ayyukansu ke nuna goyon baya ko yin wani abu da bai wa ɗan takarar APC nasara a zaɓen 2027,” a cewar sanarwar.

PDP ta ce hakan ya saɓa wa dokokin da suka kafa jam’iyyar, kuma barazana ce ga ci gaba da wanzuwar jam’iyyar.

Karanta Wannan  Likitoci a Legas sun fara yajin aiki saboda rage musu albashi

Jam’iyyar ta kuma ce hakan zai kawo tarin matsalolin da za su haifar da rarrabuwar kawuna a cikinta, wanda kuma cewarta idan ba a magance su ba za su janyo wa jam’iyyar rashin nasara a zabukan da ke tafe.

Kan haka ne PDP ta yi gargadin sanya takunkumai masu tsauri ga mambobinta da aka kama da wannan laifi.

Yanzu haka dai Nyesom Wike – wanda babban jigo ne a jam’iyyar ta PDP – na cikin ƙunshin ministocin Shugaba Tinubu na APC.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *