Tuesday, January 7
Shadow

PDP ta nemi Tinubu ya yi bincike kan tiriliyan 25 da ta zargi ‘yan APC da sacewa

Babbar jam’iyyar adawa a Najeriya ta PDP ta nemi Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ƙaddamar da bincike kan kuɗaɗe naira tiriliyan 25 da ta zargi ‘yan jam’iyyarsa ta APC da sacewa.

PDP ta yi wannan kira ne a saƙon da ta wallafa na sabuwar shekara, wanda kakakinta na ƙasa Debo Ologuagba ya sanya wa hannu ranar Talata.

“Ya kamata shugaban ƙasa ya wanke kansa game da yaƙi da cin hanci da rashawa ta hanyar ba da umarnin yin bincike da kuma dawo da sama da tiriliyan 25 da aka ce shugabannin APC da jami’an gwamnati sun sace,” in ji sanarwar.

Jam’iyyar ta kuma nemi shugaban ya bayyana adadin kuɗaɗen da gwamnatinsa ta tara daga cire tallafin man fetur da ya yi a watan Mayun 2023.

Karanta Wannan  Kungiyar kare hakkin Musulmi ta Murik ta jawo hankalin musulmai da kada su shiga yajin aiki

Haka nan, PDP ta nemi Tinubu ya kawo ƙarshen matsalar tsaro, da yunwa, da kuma ƙarancin man fetur “domin sauƙaƙa wa rayuwar ‘yan Najeriya”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *