
Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya, NBA ta bayyana cewa, Rikicin jihar Rivers bai kai matakin da za’a ce a saka dokar ta baci ba.
Kungiyar a sanarwar data fitar bayan da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya saka dokar ta baci a jihar Rivers tace tabbas kundin tsarin mulki ya baiwa shugaba Tinubu damar saka dokar ta baci.
Amma kamin a saka dokar ta baci akwai ka’idojin da ake bi.
Wasu daga cikin ka’idojin sune kamar haka:
Ya zama cewa, Ana yiwa Najeriya barazana ta bangaren jihar daga kasar waje.
Ya zama ana fuskantar barkewar yaki.
Ya zamana cewa babu doka kowa na abinda ya ga dama.
Ya zama cewa, Najeriya na fuskantar rugujewa.
Ya zama cewa wani iftila’i kamar girgizar kasa ko Ambaliyar ruwa me muni ta fadawa jihar.
Ko kuma wata matsala da ka iya shafar duka Najeriya.
NBA tace rikici tsakanin ‘yan majalisa da gwamnan bai kai matakin da ya kamaya ace an saka dokar ta baci ba, abune wanda ya kamaya a warwareshi ta hanyar zuwa kotu.