
Rahotanni sun bayyana cewa, Wani Jirgi marar Matuki ya fadi a dajin jihar Naija.
Lamarin ya dauki hankula da saka fargaba a zukatan mutane.
Musamman ma saboda harin da kasar Amurka ta kawo Najeriya a jihar Sokoto a kwanakin baya.
Saidai sabbin bayanan da ake samu game da jirgin shine cewa, na sojojin saman Najeriya ne dake tattara bayanai daga Tshàgyèràn Dhàjì.
Me magana da yawun hukumar sojojin saman Najeriya, Air Commodore Ehimen Ejodame ya tabbatar da hakan.
Yace jirgin yana tattara bayanai ne daga Tshàgyèràn Dhàjì a yayin da ya fadi inda yace amma bai kashe kowa ba ko jikkata kowa ba.
Yace amma cikin hadin gwiwa da sauran abokan aikinsu, an dauko jirgin daga inda ya fadi.