Gwamnatin tarayya ta umarci shuwagabannin sojoji da su koma jihar Sokoto da zama.
Hakan na zuwa ne yayin da matsalar tsaro musamman ta garkuwa da mutane ke kara kamari a yankin arewa maso yamma.
Sanarwar hakan na kunshene a cikin bayanan da sakataren yada labarai, Henshaw Ogubike ya fitar.
Yace wannan kokari ne na kawar da matsalar ta’addanci da garkuwa da mutane da sauran matsalolin tsaro da ake fama dasu a yankin.
Gwamnatin ta bayyana takaici da matsalar tsaron da ta ki ci ta ki cinyewa a yankin na Arewa maso yamma inda tace wannan mataki alamu ne na daukar matsalar da muhimmanci da gwamantin ta yi.