Friday, December 5
Shadow

‘Safiya ce mai wahala da kuma baƙin ciki’ – Shugaban Isra’ila

Wannan safiya ce mai baƙin ciki da kuma wahala,” kamar yadda shugaban Isra’ila Isaac Herzog ya wallafa a shafin X, a daidai lokacin da ƙasar ta wayi gari da hare-haren da Iran ta kai tsakiyar ƙasar da kuma yankuna da ke arewaci.

Hare-haren Iran “masu muni” sun kashe tare da jikkata “Yahudawa da Larabawa, ƴan Isra’ila da kuma baƙin haure, ciki har da yara da tsofaffi, mata da maza,” in ji Herzog.

Ya ƙara da cewa: “Ina makoki da kuma jajantawa iyalan da suka rasa ƴan uwa. Ina addu’ar samun lafiya ga waɗanda suka jikkata da kuma gano mutanen da suka ɓata. Za mu yi makoki tare. Za mu yi nasara tare.”

Karanta Wannan  A biya mu haƙƙoƙinmu, ba mu son bashin gwamnati - ASUU

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *