Sai kun yi nadamar komawa APC, Kwankwaso ga su Kawu Sumaila.

Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP a zaben 2023, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa ‘yan majalisar tarayya da aka zabe su a karkashin jam’iyyar NNPP da suka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki, za su yi nadamar wannan matakin da suka dauka.
DAILY NIGERIA ta rawaito cewa wasu daga cikin ‘yan majalisar da suka fito daga NNPP sun sauya sheka zuwa jam’iyyar APC a kwanan nan.
Cikin wadanda suka koma APC akwai Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Kawu Sumaila, da Alhassan Rurm, da sauransu.
Sai dai lokacin da ya ke jawabi ga daruruwan magoya bayan NNPP daga karamar hukumar Takai, wadanda su ka ƙi bin Kawu Sumaila zuwa APC, amda suka kai masa ziyara a gidansa a ranar Juma’a, Kwankwaso ya bayyana sauya shekar da cewa cin amana ce a siyasa.
Ya ce: “Kano ta Kudu ta zama darasi. Masu kada kuri’a sun ki karbar Taliya, Naira dari biyu da Atamfa, suka yi hakuri suka zabi NNPP.”
“Amma wadanda suka ci zabe a cikinmu sun zabi su bar talakawa su shiga sahun wadanda ba su damu da talakawa ba, sai dai abin da za su amfana da shi da iyalansu.”
“Babu wani babban zunubi a siyasa fiye da barin jam’iyyar da ta ba ka dama da goyon baya, amma daga baya ka juya mata baya. Wannan shi ne mafi girman cin amana,” in ji Mista Kwankwaso.