Friday, December 5
Shadow

Sakamakon WAEC na wannan shekarar shine mafi muni da aka taba gani cikin shekaru 5 da suka gabata, saboda mafi yawan daliban sun fadi

Rahotanni sun bayyana cewa, Sakamakon jarabawar WAEC na wannan shekarar shine mafi muni da aka taba gani cikin shekaru 5 da suka gabata.

A jiya ne dai WAEC ta sanar da sakin sakamakon jarabawar, saidai bayan dubawa, da yawan dalibai basu ci jarabawar ba, musamman Turanci da lissafi.

Rahoton yace daga cikin dalibai guda 1,969,313 da suka rubuta jarabawar guda 754,545 ne kadai suka samu sakamakon 5 credit wanda ya hada da Turanci da Lissafi.

Hakan na nufin kaso 38.32 ne na daibai da suka rubuta jarabawar suka ci.

Rahoton Yace idan aka kwatanta da shekarar 2024, daliban bana sun fdi jarabawar sosai.

Karanta Wannan  An Ba Su Madarar Yougot A Matsayin Gwarazan 'Yan Wasa A Wasannin Gasar Kwallon Ta Birnin Kudu Dake Jihar Jigawa

Sannan an rike sakamakon dalibai guda 192,089 saboda zarge-zargen daban-daban.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *