Friday, December 5
Shadow

Sam bana jin dadin Abinda ke faruwa a kasarnan, duk sanda naji labarin an Shekyen mutane sai na zubar da hawaye>>Inji Kakakin majalisar Dattijai Godswill Akpabio

Kakakin majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio ya bayyana cewa baya jin dadin abinda ke faruwana kasarnan.

Yace Gwamnatin tarayya ce ke da alhakin samar da tsaro a kasarnan, babu wani bako daga kasar waje da zai zo ya iya samar da tsaro a Najeriya.

Akpabio ya bayyana hakane a Jos yayin karbar wasu mutane da suka koma jam’iyyar APC.

Yace yana fatan Allah ya taimakesu su da suke tare da gwamnatin tarayya su samu su sauke nauyin dake kansu na son kawo zaman Lafiya a jihar Filato.

Karanta Wannan  Babban Ministan tsaron Nijeriya, Muhammad Badaru ya sauka jihar Filato, domin jajanta wa iyalan wadanda suka rasa ransu sakamakon harin ta'addanci

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *