
Tauraruwar Mawakiyar Kudu Tiwa Savage ta bayyana cewa samun mijin aure akwai wahala.
Ta bayyana hakane a wata sabuwar hira da aka yi da ita inda take cewa, ita wanda zai dace da ita sai ya kai shekaru akalla 50.
Tace to dole zai kasance me mata kuma a shirye take ta zama mata ta biyu, kuma zata yi kokarin su zauna lafiya a matar mijin nata.
Tace tana da girmamawa kuma zata kiyaye duk wasu sharuda da za’a gindaya mata.