
A ci gaba da dambarwar data kunno kai tsakanin kakakin majalisar dattijai, Sanata Godswill Akpabio da Sanata Natasha Akpoti inda ta zargeshi da neman yin lalata da ita, Sanata Akpabio yace Akpoti na saka kaya shara-shara.
Akpabio ya bayyana hakane ta bakin babban hadiminsa, Mfon Patrick wanda ya rubuta a shafin Facebook cewa, Sanata Natasha Akpoti ta sha aikin sanata shine yin kwalliya a koda yaushe da kuma saka kaya masu shara-shara dake nuna tsiraici.
saidai lauyan Sanata Natasha Akpoti, Victor Giwa ya shigar da kara kotu akan lamarin inda yake karar hadimin na Akpabio Patrick da shi Akpabio din da kansa inda yace wadannan kalamai sun zubarwa da wadda yake wakilta mutunci a idon jama’a.