
A ci gaba da tonon silili da Sanata Natasha Akpoti daga jihar Kogi ke yiwa kakakin majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, tace yakan kirata da sarauniyar Majalisa.
Ta bayyana hakane a wata hira da aka yi da ita inda aka bata dama ta bayyana duka zarge-zargen da takewa Sanata Akpabio.
Ta kara da cewa a baya ya taba ce mata ta daina magana kamar suna gidan rawa.
Tace wannan ba maganace ta haka kawai ba, dama ya taba ce mata zai hada musu chasu ita dashi su ji dadi idan ta yadda yayi lalata da ita.