Friday, December 5
Shadow

Sanata Barau ya ce zai goyi bayan ƙirƙiro jihar Karaɗuwa

Mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Barau Jibrin ya ce zai yi aiki tare da Sanata Muntari Dan-Dutse mai wakiltar yankin Funtua na jihar Katsina domin tabbatar da ƙirƙiro jihar Karaɗuwa daga jihar Katsina ta arewa maso yamma, kamar yadda tashar Channels ta ruwaito a shafinta na intanet.

Ya ce ƙirƙiro sabuwar jiha zai taimaka wajen ci gaba da haɓaka tattalin arzikin yankin da mutanenta.

“Zan yi aiki tare da ɗan’uwana, Sanata Muntari Dan-Dutse domin ganin an ƙirƙiri jihar ta Karaɗuwa daga jihar Katsina. Yankin Karaɗuwa na da duk abin da ake buƙata domin zama jiha. Ina goyon bayan buƙatar nan ta mutanen yankin duk da cewa lamari ne mai wahala,” in ji shi.

Karanta Wannan  Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un: Kalli Bidiyon yanda wata matashiya daga Arewa ke rikici da wani da ta ce ya aikata Alfasha da ita bai biyata ba

Barau ya bayyana haka ne a lokacin da yake jagorantar rabon tallafin kayan abinci na azumi ga dubban ƴan yankin wanda Sanata Muntari ya ɗauki nauyi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *