
Sanata Natasha Akpoti ta ki mikewa tsaye kamar kowane ‘yar majalisa bayan da kakakin majalisar, Sanata Godswill Akpabio da take zargin ya nemi yin lalata da ita ya shiga majalisar.
A daidai wannan lokacin, bulaliyar majalisar, Sanata Mohammed Monguno ya gargadi sanata Natasha Akpoti da cewa dokar majalisar ce idan kakakin majalisar na shiga kowa sai ya mike.
Ya jawo hankalinta da cewa ya kamata ta rika mutunta dokar majalisar ba tare da la’akari da wani abuba.