
Sanata Neda Imasuen daga jihar Edo na shirin komawa jam’iyyar APC daga jam’iyyar Labour Party.
Hakan na faruwa ne yayin da ake ganin yana hada alaka me kyau da ‘yan APC a jihar ta Edo kamar yanda kafar jaridar Vanguard ta ruwaito.
Hakanan Rahoton yace Gwamnan Edo, Monday Okpebholo ya aike da wakilinsa me bashi shawara a harkar siyasa dan ya kara jawo Neda Imasuen ya shiga jam’iyyar sa.