
Sanata Neda Imasuen daga jihar Edo ya bar jam’iyyar Labour Party inda ya koma jam’iyyar APC inda yace rikicin cikin gida ya mamaye jam’iyyar ta APC.
Ya bayyana ficewarsa daga Labour party zuwa APC a zaman majalisar Dattijai na ranar Laraba.
Kakakin majalisar, Godswill Akpabio ne ya sanar da hakan inda ya karanto takardar da sanata Nedu ya aikawa majalisar.
Yace kamin yanke wannan shawara sai da ya tuntubi da yawa daga cikin abokan shawararsa da mutanen mazabarsa da sauransu.