
Mai alfarma sarkin Musulmin Najeriya, Muhamad Sa’ad Abubakar III na sanar da fara duba watan Ramadan daga gobe Juma’a 28 ga watan Sha’aban, wanda ya yi dai dai da 29 ga watan Janairun 2025.
Cikin wata sanarwa da shugban kwamitin harkokin addini na fadar mai Alfarmar, Farfesa Sambo Wali Junaidu ya fitar ranar Alhamis ya ce idan aka ga watan a sanar da fadar mai alfarmar ta hanyar wasu lambobin waya da ya bayar.
Sanarwar ta ƙara da cewa idan ba a ga watan a ranar Juma’a ba, to ranar Lahadi za ta kasance 1 ga watan Ramadan na wannan shekara.
A ranar Laraba ne dai hukumomin Saudiyya suka da fara duba watan Ramadan ɗin daga gobe Juma’ar.