
Babban yaron Naziru Ahmad Sarkin Waka, Abba C Sale ya bayyana cewa, Sarautar Sarkin Wakar kasar Hausa da aka baiwa Rarara ba ta inganta ba.
Yace sarkin Daura ne ya bayar da Sarautar dan haka a Kano su ba zasu kira Rarara da Sarkin Wakar Kasar Hausa ba.
Yace Sarkij wakar Daura da Katsina ne Rarara.
Hakan na zuwane jim kadan bayan da Me Martaba sarkin Daura, Umar Farouk Umar ya nada Rarara a matsayin sarkin Wakar kasar Hausa.