
Kungiyar Kare muradin yarbawa ta Afenifere ta bayyana cewa, shugaban kasar Amurka, Donald Trump zai shigo Najeriya ne da niyar satar arzikin kasa amma ba maganar tseratar da Kiristoci ba.
Kungiyar ta bakin sakataren yada labarinta, Mr. Jare Ajayi tace hujjar da Trump ya kawo ta banza ce kawai yana neman hanyar shigowa Najeriya ne.
Yace Trump na son amfani da wannan damar ne wajan tilasta Najeriya sayen abubuwa daga Amurka musamma makamai saboda baya jin dadin huldar da Najeriya ke yi da kasar China.
Yace sannan Amurkar ta ji haushin kalaman da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima yayi a taron majalisar Dinkin Duniya inda ya goyi bayan kafa kasar Falasdiynawa.
Kungiyar ta yi kira ga ‘yan Najeriya dama shuwagabannin da su kaucewa yin kalaman da zasu kara zhugha Amurka tace zata shigo Najeriya inda tace babu kasar da Amurka ta shiga da ta kare da samun zaman Lafiya.