
An haramta wa mazan Saudiyya auren matan Pakistan, Bangladesh, Chadi, da Burma.
Jaridar Gulf News ta rawaito cewa an bayyana matakin ne domin hana mazan Saudiyya aurar mata ƴan kasashen waje.
Jaridar ta rawaito cewa ƴan kasar Saudiyya da ke son auren mata daga kasashen waje sai sun fara samun amincewa daga hukumomin gwamnati da abin ya shafa sannan su mika takardar neman aure ta hanyoyin hukuma.
Manjo Janar Assaf Qureshi, wanda shi ne daraktan ƴan sandan Makkah ya ce dole sai duk wata bukata ta aure daga wajen masarautar ta bi ta hanyoyi da wasu sharudda kafin a ba da izini ko kin amincewa.
Har ila yau, dole ne a yi la’akari da cewa don ɗaukar matakin sanya dace, kwamitin yana buƙatar lokaci mai tsawo don aiwatar da aikace-aikacen sa.