Saturday, March 15
Shadow

SAUKIN RAYUWA: Farashin Man Fetur Ya Ƙara Zaftarowa Kasa A Nijeriya

A wani yanayi na ƙara raguwar farashin kayan masarufi da abeben more rayuwa a Najeriya,
Kamfanin Man Fetur na NNPCL, ya sanar da rage farashin man fetur daga Naira 920 zuwa Naira 860 kan ko wace lita.

Wannan raguwar farashin ya biyo bayan rige-rigen sauke farashin kayayyaki dake gudana tsakanin yan kasuwanni wanda bai bar har dilolin man fetur ba, sakamakon tashin darajar Naira da ta fetur a kasuwannin duniya

Sabon farashin kamfanin na NNPC, zai fara aiki a ranar Litinin mai zuwa.

A makon da ya gabata ma, matatar mai ta Dangote ta rage farashin man fetur daga naira 890 a kowace lita zuwa naira 825, wanda hakan ya zamo karo na biyu da take rage farashin a wata ďaya kacal.

Karanta Wannan  Mun daina fargabar da muke yi akan Muslim-Muslim saboda Gwamnatin Tinubu ta mana Adalci>>Inji Kungiyar Kiristanci ta CAN

A cikin sanarwar rage farashin da Kamfanin da na NNPCL ya fitar, ya sanar da wasu abokan huldarsa guda uku da za su fara sayar da mai akan sabon farashin a jahar Legas wanda suka hada da MRS mai sayarwa a kan Naira 860, sai AP a kan Naira 865, sai kuma Heyden a kan Naira 865 kowace lita.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *