Friday, December 5
Shadow

Shaguna kusan 500 ne suka ƙone a kasuwar Terminus ta Jos

Shaguna kusan 500 ne suka ƙone ƙurmus sanadin tashin gobara a babbar kasuwar Jos da aka fi sani da Terminus a jihar Filato ta tsakiyar Najeriya.

Yankasuwar sun ce gobarar ta tashi ne da tsakar daren jiya Talata kuma sun yi asarar dukiya ta miliyoyin naira.

Hukumar agajin gaggawa ta Najeriya Nema ta ce mutum 309 ne shuganansu suka ƙone tare da kayan ciki, sai wasu 58 da ‘yandaba suka wawashe.

Mustapha Ibrahim Bako, shi ne shugaban kasuwar ta Terminus kuma ya faɗa wa BBC cewa rashin zuwan motocin kashe gobara da wuri ne ya jawo ta’azzarar ɓarnar.

“Halin da ake ciki babu daɗi, a jiya mun kwashe mutane sun fi 10 saboda hayaƙin da suka shaƙa, wasu kuma firgici,” in ji shi.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Ni zan iya yin soyayya da maza 10 kuma kowanne ina sonsa>>Inji Wannan matashiyar

Ya nemi gwamnatin jihar da “kada ta ce za ta kori kowa a kasuwar, saboda akwai wuraren da wutar ba ta shafa ba, a ƙyale su su ci gaba da kasuwancinsu”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *