
Shaida ya gayawa kotun tarayya dake Abuja cewa, Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahya Bello bashi da hannu game da maganar sayen gidan Naira Miliyan 550 a Maitama Abuja.
Sannan an gayawa kotun cewa, duka takardun sayen gidan basu dauke da sunan Tsohon Gwamnan.
Shaidan da ya bayar da wannan bayani na hukumar EFCC ne.
Shaidan EFCC me suna Olusegun Joseph Adeleke wanda dillalin gidajene lauyan EFCC Kemi Pinheiro, SAN ne ya kawoshi.
Shaidan yace shugaban kamfaninsu, Fabian Nwora ne ya kirashi suka yi zaman tattaunawa da wanda zai sayi gidan na Naira Miliyan 550 me suna Shehu Bello.
An tambayeshi yayin cinikin ko ya ga Tsohon Gwamnan jihar Kogin inda yace bai ganshi ba.
Saidai yace bayan an kammala ciniki, Shehu Bello ya biya kudin gida, daga baya ya koma inda ya nemi a bashi kudinshi saboda ya gano hukumar EFCC na bincike akan gidan.
Shaidan na EFCC ya bayyana cewa, akwai kuma wani mutum me suna Nuhu Mohammed wanda shima ya je wajensa ya sayi gida a Gwarimpa na Naira Miliyan 70.
Kotun ta dage sauraren karar sai zuwa ranar 6 da 7 ga watan Maris dan ci gaba da saurare