Friday, December 5
Shadow

Sharudan da aka gindaya min kamin a mayar da ni Gwamna basu da dadi amma na amince>>Inji Fubara

Dakataccen Gwamnan jihar Rivers, Simi Fubara ya bayyana cewa, Sharudan da aka gindaya masa ya cika kamin a mayar dashi kan kujerar gwamna basu da dadi.

Yace amma ya amince dasu.

Fubara ya bayyana hakane a yayin ganawa da kungiyar masoyansa inda yace musu su amince da sharadin suma domin indai ba rayuwarsa aka ce ya bayar ba zai amince da duk wani sharadi dan dai a zauna lafiya.

Fubara ya bayyana cewa, suna godiya da irin rawar da Wike ya taka wajan ci gaban jihar da kawo karshen rikicin jihar.

Wasu daga cikin sharudan da aka gindayawa Fubara sune dole ya amince ba zai sake tsayawa takara a zaben shekarar 2027 ba sannan zai biya ‘yan majalisar jihar hakkokinsu da ya dakatar, sannan Wike ne zai tsayar da ‘yan takarar kananan hukumomi a jihar.

Karanta Wannan  Ganin Bidiyon matar Rarara ta 3 ya dauki hankulan mutabe sosai ana ta san barka

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *