Friday, December 5
Shadow

Sheikh Ɗahiru Bauchi dattijo ne mai son zaman lafiya – Kwankwanso

Tshon ɗan takarar shugaban Najeriya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana jimaminsa tare a miƙa ta’aziyya ga iyalai da ƴanuwan da makusantan Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi bisa rasuwar malamin.

Kwankwaso ya bayyana malamin a matsayin uba, kuma babban malami wanda koyarsa ta zama madubi ga ɗimbin al’umma.

“Ta hanyar karantarwa, Sheikh Ɗahiru taɓa rayuwar al’umma da dama tare da jan hankalinsu wajen koyi da halaye masu kyau da kuma ƙaunar Alqur’ani da sunnar manzon Allah.”

Kwankwaso ya ce shehin mutum ne mai son zaman lafiya kuma dattijo mai ƙoƙarin haɗa kan ƴan ƙasa, “wanda kuma ba za mu manta da shi ba, kuma ƙasarmu ba za ta manta da shi.”

Karanta Wannan  Abu ya girmama, Kalli Bidiyon yanda Tauraron fina-finan Hausa, Saheer Abdul ke bin Adaidaita da gudu yana sayar da garin Danwake

“A madadin iyalina da ni kaina, ina miƙa ta’aziya da iyalansa da ɗalibansa da gwamnati da al’ummar Bauchi bisa wannan rasuwa. Allah ya saka shi a aljanna.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *