
An kama wani me sana’ar sayar da sassan jikin dan Adam me suna Gani a yankin Kulanla Odomoola na jihar Ogun.
Sojoji na runduna ta 81 ne suka kamashi a yayin da mutane suka rufar masa da duka ana shirin kasheshi.
Ya amsa laifinsa inda yace shekara goma kenan yana wannan sana’a.
Ya kara da cewa, yakan samu sassan jikin dan Adam ne a makabartu da kuma idan an yadda gawa.
Ko yanzu ma da asirinsa ya tonu, an kamashi ne yana shirin kaiwa wani abokin huldarsa sassan jikin dan Adam ne.
Me magana da yawun sojin, Lieutenant Colonel Olabisi Olalekan Ayeni, ya tabbatar da kamen inda yace sun mikashi hannun ‘yansanda.