Wednesday, January 7
Shadow

Shekarata 31 a masana’antar Fim amma babu wanda na yadda ya taba yin lalata dani

‘Yar fim din kudi, Thelma Chukwunwem ta bayyana cewa shekararta 31 tana fim amma babu wani darakta ko Frodusa da zai ce ya taba kwanciya da ita.

A hirar da aka yi da ita a Jaridar Vanguard tace a lokacin da ta fara fim an ta kai mata harin neman yin lalata da ita amma ta ki yadda.

Tace akwai daraktan da ya taba gaya mata ba zata ci gababa tunda bata basu hadin kai amma ita ta bashi amsar cewa Allah zai taimaketa.

Ta alakanta hakan da tarbiyyar data samu a gida.

Karanta Wannan  Kasar Burkina Faso ya dakatar da shigar mata da kayan Gwanjo daga kasar Amurka

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *