Thursday, December 25
Shadow

Shirmenshi ne kawai, Majalisar mu Bata amincewa Trump ya kawo Khari Najeriya ba>>Inji ‘Yar Majalisar Kasar Amurka, Sara Jacobs

‘Yar majalisar kasar Amurka, Sara Jacobs ta bayyana cewa babatun da shugaban kasar, Donald Trump ke yi na cewa, zai kawo Hari Najeriya shirme ne kawai.

Tace dalili kuwa sai majalisa ta amince kuma majalisar bata amince maza ba.

Tace sannan wannan magana ta rashin dacewa da Trump yayi maimakon ta taimaka, sai ma kara dagula lamura ta yi tsakanin Kiristoci da Musulmai a Najeriya

Tace kuma kawo Hari a Najeriya ba tare da amincewar gwamnatin Najeriyar ba abune wanda zai sabawa dokar kasa da kasa.

Tace kuma kawo Hari zai shafi fararen hula da yawa.

Tace dan haka abinda yafi shine a bi hanyar Diplomasiyya dan warware wannan matsala.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon Allah Sarki: Shekara daya kenan da daukar Bidiyon a yayin da ake taya tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari murnar cika shekaru 82 a Duniya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *