Friday, December 5
Shadow

Shugaba Tinubu ya aika Kashim Shettima ya duba Buhari a Landan sannan ya gano wane hali yake ciki? Ji Halin da Kashim ya tarar da Buhari a Landan

{“remix_data”:[],”remix_entry_point”:”challenges”,”source_tags”:[],”origin”:”unknown”,”total_draw_time”:0,”total_draw_actions”:0,”layers_used”:0,”brushes_used”:0,”photos_added”:0,”total_editor_actions”:{},”tools_used”:{},”is_sticker”:false,”edited_since_last_sticker_save”:false,”containsFTESticker”:false}

Shugaban kasa Bola Tinubu ya aika mataimakinsa, Kashim Shettima ya duba tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari a landan.

A baya dai an samu rahotanni masu cewa, tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari na can kwance a Landan kasar Ingila bashi da Lafiya.

Rahoton yace Shugaba Tinubu ya aika da Kashim Shettima bayan gaishe da Buhari ya kuma dubo masa da halin da tsohon shugaban kasar ke ciki.

A baya rahotanni sun ce an kai tsohon shugaban kasar bangaren kula da marasa lafiya na musaman.

Ranar Litinin ne Kashim Shettima ya gana da Buhari a landan sannan kuma ya hada Buharin da shugaba Tinubu.

Saidai Rahoton yace fadar shugaban kasar ta ki bayyana labarin inda alamu ke nuna an so a boyeshi ne.

Karanta Wannan  Sai mun biya Naira Miliyan 3 ake yadda mu gabatar da kudirin doka a majalisa>>Inji Dan majalisar tarayya Hon. Ibrahim Usman Auyo

Rahotan ya kuma ce bayan Buhari, Kashim ya kuma gana da tsohon shugaban kasa, Abdulsalam Abubakar wanda ke can landan din shima yana jinya.

An tuntubi me taimakawa shugaban kasa kan sadarwa, Stanley Nkwocha game da lamarin inda yace tabbas Kashim Shettima ya je Landan amma bai da masaniyar ganawarsa da Buhari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *