
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya godewa Majalisar tarayya bisa amincewa da dakatar da gwamnan jihar Rivers, Simi Fubara da yayi.
Shugaban yace yana godiya musamman ga shuwagabannin majalisar, Kakakin majalisar Dattijai Godswill Akpabio dana majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas.
Sannan yace yana godiya ga sauran manyan ‘yan majalisar dama duka ‘yan majalisar.
Shugaban ya kuma ce yana godiya ga ‘yan Najeriya da suka bashi goyon baya bisa wannan lamari.
Ya bayyana cewa yana fatan nan da wata 6 din da aka dakatar da gwamnan da majalisar a samu sulhu tsakanin wadanda basa jituwa.
Shugaba Tinubu yace fadan jihar Rivers yana barazanane ga tattalin arzikin Najeriya shiyasa suka dauki matakin da suka dauka.
Ya sha Alwashin ci gaba da hada kai da majalisar tarayya dan kawo ci gaba a kasa.