
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya yi Allah wadai da kashe-kashen da suka faru a Najeriya musamman a jihohin Benue, Filato da Borno.
Shugaban yace a yiwa tsarin tsaron kasar garambawul inda yace abin ya isa haka.
Babban me baiwa shugaban kasar shawara akan harkar tsaro, Malam Nuhu Ribadu ne ya bayyana hakan i da yace yayin ganawar, shuwagabannin tsaron sun baiwa shugaba Tinubu bayanai kan yanda lamarin tsaron ya kasance.
Yace shugaba Tinubu ya kuma bayar da umarnin a canja salo game da yanda ake yaki da matsalar tsaron.