Friday, January 9
Shadow

Shugaban APC, Ganduje yayi magana bayan cece-kuce yayi yawa kan Bidiyon da aka ga dansanda na gyara masa takalmi

A jiyane Bidiyo ya bayyana inda aka ga Shugaban jam’iyyar APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje a tsaye, dansandansa ya duka yana daure masa takalmi.

Bidiyon ya watsu sosai a kafafen sada zumunta inda akaita bayyana mabanbanta ra’ayoyi akai.

Da yake mayar da martani kan lamarin ta bakin kakakinsa, Aminu Dahiru Ahmad, Ganduje yace wasu ne dake son jawo cece-kuce da kawo rudani a tsakanin al’umma suka fitar da Bidiyon.

Yace Ganduje an sanshi mutum ne me haba-haba da mutane sannan kuma yana da kyakkyawar alaka tsakaninsa da masu masa aiki shiyasa aka ga abinda dansandan yayi.

Karanta Wannan  Kalli Yanda a Maulidin Bana, Sheikh Qaribu Kabara Ya kawo tsarabar Reshen Itaciyar Annabi Adamu(AS)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *